Tsuguni-tashi bata kare ba, a yayin da Mal. Kabiru yake jin jiki ga shi kuma asibitoci na tsaka da yajin aiki, bug da kari ba kudi a hannun su Alawiyya. Madina da Zuby baki har baka don sun tare a sabon gida. Kakar Rambo tana cikin rashin lafiya, ga kuma Rambo bayanan. A bangare guda su Badaru da Wizzy sunyi abin kirki, amma fa Ojukwu ya sasu a kwana. Anya kuwa asirin Timo bai gama bankaduwa ba?