Lamarin Aminu da Kamal ya kai matuka, domin har sun fara Sa’insa da Babban malamin garin Dadin kowa, shin me wadan nan matasan suka taka haka. Yayin da a gefe guda kuma Gimbiya ta fara fuskantar gagarumar matsala ta zamanta gidan Mal. Kabiru. A Bangaran Stella kuma ta kara budewa Patrick wuta akan neman ‘Danta, shin Yaya Patrick zai yi da Ita ne? domin ganin yanda wannan turka-turka za ta kaya, ku kalli shirin Dadin kowa.